Posts

Showing posts from December, 2018

(Ka Duba Sunanka) Nigerian Army Ta Saki Sunaye.

Image
Hukumar Sojan Kasa ta Najeriya (Nigerian Army) ta saki sunayan wanda ta ɗauka a rukunin: *Short ServiceCombatant Commission (SSC) 45/2019 da kuma *Direct Short Service Commission (DSSC) 24/2019.
Za afara tantancewa a aranar 14 zuwa 18 na watan January 2019. 
Za atantance (SSC) a Old Site Mando Kaduna, Kaduna State.
(DSSC) kuma a 20 Battalion Barracks, Serti Baruwa, Taraba State.
Shiga kasa ka duba Sunanka https://nigerianarmymsng/

YADDA DALIBAN BUK ZASU NEMI AIKIN ZABE INEC 2019

Image
Yadda Daliban BUK Zasu Nemi Aikin Zabe INEC 2019

Shugaban kungiyar dalibai ta kasa reshen jami’ar Bayero dake Kano yana sanar da dalibai ‘yan Jami’ar cewa ga duk wanda yake da sha’awar yin aikin zabe na shekarar 2019 da suje ofishin al’amuran dalibai na Jami’ar Bayero Ranar Litinin 31, December, 2018 domin karbar foam da zasu cike.Ana bukatar dalibi yaje da ID Card dinsa.

Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa zata debi ma’aikata na wucin gadi kimanin Dubu Arba’in Da Shida 46,000 domin gudanar da zaben w
2019.

Allah ya bada sa’a.


Sanarwa daga shuwagaban kungiyar dalibai na Jami’ar.

Source: edu.sharfadi.com

Nisabin Zakkah, Sadaki Da Diyyah.

Image
Daga Shafin Kwamitin Duban Wata (National Moon Sighting Committee)  Na Majalisar Koli Ta Harkokin Addinin Musulunci Ta Najeriya (National Supreme Council Of Islamic Affairs).ZAKKAH UPDATE
20TH  RABI'UL-THANI 1440AH
28TH DECEMBER, 2018

Minimum Zakkah Nisab (Gold):N1,168,720:00

Haddin sata/Sadaki/ Dowry/ Theft: N14,609

Diyyar/Blood Money: N58,436,000

 source :Islamic timing and research org.

 08033140010/ 07032558231

Wata ɗalibar ABU Zaria ta kashe kanta.

Image
Wata ɗalibar Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria (ABU) ta kashe kanta. Dalibar me suna Aisha Abdulganiyu dake tsangayar Library and Information Science.

Dalibar yar aji uku ce (Level 300) kuma itace mataimakiyar shugaban aji (Assistant Class Rep).
Ta mutu ne bayan ta ɗaɗɗaki guba, wadda ita ce sanadiyar mutuwar ta ta, kuma ta rubuta wasika, inda ta bayyana dalilinta na ɗaukar wannan mataki.Ta bayyana a cikin wasikar cewa iyayanta sune sanadiyar mutuwar ta,  saboda matsin lamba da take samu daga gare su, duk da kokarin da take na ganin ta kyautata musu, kuma ɗan uwanta shine yake ɗaukar ɗawainiyar karatun ta.
Daga karshe, ta bawa Yan uwa da Kawayanta hakuri na rashin ɗaukar Kaddarar ta.

Ta bayyana lambar sirri ta waya da bankin ta da adadin kudin da ke ciki.
Phone password : 3456
Atm pin: 1997
Amount: 12,000 Naira.

Ko kuna ganin wannan Shi ne matakin da ya dace ta ɗauka?

Yadda Ake Canja Salon Rubutu A WhatsApp

Image
Ana Yi Muna Jin Dadi 038

Yadda Ake Canja Salon Rubutu A WhatsApp

www.sharfadi.com

Bayan gaisuwa da fatan kowa yana lafiya, yau a darasin mu na ANA YI MUNA JIN DADI zamu yi magana akan Yadda Ake Canja Salon Rubutu A WhatsApp, sai a biyo mu.

Idan kana so ka kumbura rubutu a WhatsApp to zaka yi amfani da alamar * ka sanya ta a farko da kuma karshen inda kake son kumburawar misali:


Ina son rubuta Basheer sai na saka Basheer+ *
amman sai na cire wannan + din zai koma *Basheer

Idan ina son na karkatar da rubutun kuma sai nayi amfani da alamar Basheer+ sai na cire + din zai koma Basheer

Idan ina so na ja layi akan rubutun kuma sai nayi amfani da alamar ~ misali ina son na saka tambarin Naira ~N+~ amma sai na cire + din zai koma ~N~

Idan ina so na canja tsarin rubutun daga wanda nake amfani dashi kuma sai nayi amfani da guda uku misali Basheer + sannan guda uku ake sakawa. Sai ka cire + zai baka ““Basheer“` .

Zamu dakata anan sai a rubutu na gaba.

Domin samun sauran rubutukan da suka gabata …

Yi Register; Ma'aikatar Ilimi ta fara bada Scholarship na shekarar 2019/2020.

Image
Ma'aikatar Ilimin Tarayyar Nigeria (Federal Ministry of Education) ta fara bada Scholarships na Shekarar 2019 /2020.

Kar kabari abarka a baya. Za arufe ɗauka a ranar 3, January 2019.

Dan yin Register se ka danna kasa.


Federal Ministry of Education Scholarship 2019/2020


Ayi share yan uwa su anfana

Yadda Zaka Dora Lambobin Wayarka Akan Google

Image
Yadda Zaka Dora Lambobin Wayarka Akan Google

Assalamu alaikum, a yau zamuyi magana akan yadda ake dora lambobin waya wato Contacts aka Google, sai a biyomu.

Menene Google Contact?
Google Contact shine tsarin adana lambobin wayarka da kuma emails na mutanenka akan Google, Wanda hakan zai baka damar samun contact dinka koda kuwa ka yarda wayarka.
Idan yanzu wayarka babu chaji kuma kana son ka dauki lambar wani daga cikin lambobinka to kawai zaka iya karbar wayar abokinka kayi login a Google dinka shikenan zaka ga lambobinka.
Kuma yana cin lambobi ba adadi fiye da layin waya.

Ta Yaya Zaka Mallaki Google Contact?


Domin samun damar amfani da google contact abinda kake bukata shine account na Google domin samun cikakken bayani akan Google Account sai ka shiga nan:
https://www.sharfadi.com/2018/11/07/shin-ko-kasan-maanar-google/

Domin sanin yadda ake bude google account kuma sai kabi nan:
https://www.sharfadi.com/2018/02/21/yadda-ake-bude-email/Bayan ka mallaki wannan account din to shiken…

(NYSC) Dan bautar kasa da aka biya shi kuɗin Allawee N198,800 amemakon 19,800

Image
Wani Dan Bautar kasa da aka turashi jahar Borno me suna Abu Bakr Bilyamin, antura masa Naira dubu ɗari da Casa'in da Takwas da ɗari Takwas 198,800, amadadin Naira dubu Shatara da ɗari Takwas 19,800,da ake biyan masu hidimar kasa Allawee.

Bayan shigar kudin Bilyamin ya aika sako a kafar sadarwa ta Twitter  zuwa ga Daraktan Hukumar NYSC game da kudin da aka tura masa.

Ga sakon:


Shin idan kai ne za ka mayar da kudin?Taza Da Tsifa Dangane Da Virus A Computer

Image
*Menene Virus a Computer?*
Virus shine kwayar cutar dake kama na’urar computer sannan take yi mata illa kamar yadda cuta take yiwa mutum illa. Virus na zuwa a tsarin code ko kuma yaren baiwa computer umarni.
Virus yana lalata bayanan da ya samu akan computer.
Masu yin kutse a na’urar computer da internet sune ke kirkirar mafi yawan virus domin su samu damar leken asirin wasu computers din.*Ta Ina Virus Yake Shafar Computer?*
Virus yana lalata programs da akayi installing (software’s) ko kuma kaya (files, document) dake kan computer.
Idan virus yakama computer ka to zaka iya shafawa sauran computer dake alaka da ita kamar ta networks ko kuma offline wajen karbar wasu bayanai daga wasu computer din.

*Ta Ina Ake Samun Virus?*
Ana samun virus a computer ta hanyoyi kamar haka:
1. Sakonnin Email & Text messages
2. Files da kake download daga internet
3. Link da kake budewa ta internet,
Ka kula da kyau kada kayi downloading a shafin da baka gasgata ba.*Alamomin Dake Nuna Virus Ya Kama…

[Wata Sabuwa] Za’a Fara Biyan Kudi Domin Saka Story A Facebook Da Messenger

Image
[Wata Sabuwa] Za’a Fara Biyan Kudi Domin Saka Story A Facebook Da MessengerA cigaba da sauye-sauyen da kamfanin facebook keyi ya kara bullo da sabuwar hanya wadda zata kawowa facebook din kudin shiga.

Facebook ya bayyana cewa nan bada jimawa ba zai bada dama ga duk mutumin da yake son isar da wani sako ta story to sai ya biya facebook kudi su kuma zasu tallata story din ta yadda wadanda yake son ya isarwa sakon zasu gani.Kamar dai yadda ake boosting Post a facebook din, ta yadda zaka biya su tallatawa jama’a.

Dandalin sada zumunta na Snap chat shine wanda ya fara kirkirar irin wannan tsari na story wanda zai baiwa mutum damar sanya wani sako wanda zai gushe bayan awanni 24, daga baya kamfanin facebook ya dauka inda ya sanyashi a WhatsApp daga bisani kuma ya kawoshi Facebook da kuma manhajar sakonni ta Messenger.


A watan da yagabata shima dandalin YouTube Ya kaddamar da irin wannan tsarin amman mai tsawon mako guda.

Izuwa yanzu dai akwai mutane sama da Miliyan Dari Uku 300,000,000 d…

YADDA ZAKAYI REGISTER BUSINESS NAME DA C.A.C AKAN N5,000 KACAL

Image
A yanzu dai gwamnati tayi rangwame kan rijista da hukumar Corporate Affairs Commission wato (C.A.C) zuwa N5,000 sabanin tsuga-tsugan kudi da ake biya a baya, kuma wannan damar har zuwa karshen watan December na wannan shekara ta 2018.


YADDA AKE YIN REGISTER DA C.A.C SHINE:

Da farko zaka fara bude account a shafinsu, yadda zaka bude kuwa shine:

Kaje https://services.cac.gov.ng
Sai ka danna “Register”
Zai bodo maka da form da zaka cike, babban abinda zaka lura anan shine, duk inda ka ga alamar “*” to dole ne sai ka cike wajen, sannan ka kula da duk abinda kake cikewa.
Daga nan zasu tura maka da sakon tabbatarwa zuwa email dinka sai kaje kayi confirming shikenan ka bude account.
YADDA ZAKA YIWA KAMFANINKA REGISTER BUSINESS NAME:


Zaka koma site din nasa
Sai kayi Login
Daga nan sai ka dan “Name Reservation”
Sai ka shiga “Classification” sannan ka danna “Private Unlimited Company”
Sai ka sanya sunan da kake son yin searching zasu baka dama ka sanya sunaye guda biyu 2 saboda idan baka samu …

[KA SHIGA KA KARANTA] JAMB TA FITAR DA RANAR DA ZA’A FARA REGISTER JAMB 2019

Image
[Ka Shiga Ka Karanta] Jamb Ta Fitar Da Ranar Da Za’a Fara Register Jamb 2019

Hukumar shirya Jarrabawar shiga makarantar gaba da Sakandire ta Jamb ta sanar da ranar da za’a fara register Jarrabawar ta wannan shekara.


A wata sanarwa da shugaban hukumar Jamb din ya bayar a yau Alhamis jim kadan bayan kammala taro na musamman da jami’an hukumar ya bayyana cewa za’a fara register Jarrabawar a ranar 11 Ga watan January na shekara Mai kamawa 2019.

A wannan shekarar dai jamb ta sanar a baya cewa za’a fara register a karshen watan October da ya gabata, sai dai hakan bai samu ba.Allah ya bada sa’a.

Basheer Sharfadi
Social Media Strategist.

[KA RANTA YANZU] ABINDA YAKAMATA KA SANI GAME DA HUKUMAR JAMB

Image
Jamb 2019/2020

Marubuci: Ismail Saleesu Ali (Arewa Students Orientation Forum)Kashi Na 01
Tarihin Hukumar Jamb:-
Joint admission and matriculation Board (JAMB)
Wannan hukuma cibiyace ta shirya jarabawar Share fagen shiga Jami,a tare da sauran cibiyoyin ilimi aduk fadin Nigeria kamar irinsu Polytechnics da Colleges, kuma mutum zaisamu damar yin jarabawar ne matukar dai ya kammala karatunsa na sakandare.
Shiga Jami,a kafin akirkiri hukumar jamb:-
Kafin akirkiri Hukumar jamb Nigeria tanada jami,O,I ne guda shida zuwa bakwai a shekarar 1974 kenan. Kowace jami,a daga cikinsu tana shirya jarabawarta ne kuma tadauki adadin daliban da sukayi Nasarar cin jarabawar. Ana cikin hakan karkashin jagorancin mulkin Chief Olusegun Obasanjo a shekarar ya kara kirkirar wasu jami,o,I guda shida (6), bayan haka kuma sai gwamnatin ta kafa wani kwamiti dazai rika kula da jarabawar ta shiga jami,a karkashin shugabancin Mr. M. S Angulu.
Bayan haka sai wannan kwamitin ya bada shawarar akafa wasu hukumomi gud…

YADDA ZAKA NEMI RANCEN KUDI N300,000 ZUWA SAMA DAGA GWAMNATIN TARAYYA –FARMER MONEY

Image
*Yadda Zaka Nemi Rancen Kudi N300,000 Zuwa Sama Daga Gwamnatin Tarayya –Farmer Money*

 *Menene Famer Money?*
Famer Money daya ne daga cikin tsarukan bada rance don bunkasa arzikin al’umma da gwamnatin tarayya ta kaddamar karkashin tsarin Government Enterprise and Empowerment Prpgramme (GEEP), ba tare da kudin ruwa ba sai dai 5% na tsarin gudanarwarsa.


*Ire-Iren tsarin GEEP:*
Tsarin bada rance na GEEP ya rabu gida uku (3) kamar haka:
Famer Moni: Yana Farawa Daga N300,000
Market Moni: Yana Farawa DagaN50,000
Trader Moni: Yana Farawa DagaN10,000


*Abubuwan Da Kake Bukata Domin Samun Rancen GEEP:*
Dole ka kasance dan Nigeria
Dole ka kasance dan shekara 18 zuwa sama.
Dole ya zama kana kasuwanci ko sana’a
Ya zama kana da register da kungiyar sana’ar da kakeyi ko ta hukuma a yankinka.
Ya zama kana da ID Card, katin Dan Kasa ko katin Zabe.
Ya Zama kana da Bank Verification Number (BVN)
Lambar waya wadda kayi register da layin da kanka.
Email Address mai aiki.


Zaka iya yin register hadaka da t…

[KARANTA YANZU] ABUBUWAN DA YAKAMATA KA SANI KAFIN KAYI REGISTER JAMB 2019

Image
Jamb 2019/2020 Kashi Na 02 Marubuci: Ismail Saleesu Ali (Arewa Students Orientation Forum) – Ranar 10th January, 2019 za’a fara Siyarda Form Na Jamb – Sati Shida Kacal za’ayi ana Siyar wa – JAMB Ba Za Ta Amince Da Ci Gaba da yin rajistar UTME (Jamb) a Kafe ba Hukumar shirya jarabawar Share fagen shiga Jami’a, wato (Jamb) ta ce za ta fara siyar da fom din na Jamb ne daga ranar 10 ga watan January, 2019. Hukumar ta Jamb ta bayyana hakan ne a lokacin wani taro da ya gudana tsakanin ta da cibiyoyin ilimin komputa da ke Jami’ar Legas, ranar Alhamis dinda ta gabata. Hukumar ta Jamb ta bayyana cewa bazata lamunci yin rajistar jamb din ba a kowanne Kafe/Cafe. Shugaban hukumar ta JAMB, Prof. Ishaq Oloyede ya ce daga yanzun ba za’a ci gaba da yin rajistan na UTME (jamb) ba a kowane cibiyoyin Cafe, sai dai a wurare na musamman da muka kebe. Prof. Oloyede, ya bayyana cewa, kayyade wuraren yin rajistan an yi shi ne ba dan komai ba sai dan a magance yanda ake chajin dalibai masu yin rajistan kudade…

[Cigaba] Yadda Zaka Magance Matsalar Shan Data Da Cinye Storage Daga WhatsApp Group

Image
[Cigaba] Yadda Zaka Magance Matsalar Shan Data Da Cinye Storage Daga WhatsApp GroupMasu amfani da dandalin sada zumunta na WhatsApp sunsha yin korafi akan yadda WhatsApp Group ke cinye musu Data da kuma Space akan waya ta yadda da zarar an turo sakon hotuna ko video to kawai sai ka ga sun hawo kan wayarka kana so ko baka so.

A baya dai mutum yana iya tsayar da sauke hoto/video kai tsaye (auto download) ta yadda sai ka danna sannan zai sauka kan wayarka.

To a yanzu dai whatsApp yazo da sabon sauyi wanda ya fara aiki a iya Group kadai.

Yadda Tsarin Yake:
Shine a yanzu da zarar an turo hoto ko video a group to zaka iya kallar abinka ba tare da ya zo kan wayarka ba ballantana ya cinye maka space sannan yana rage shan Data sosai.

Yadda Ake Shiga Tsarin Shine:
Idan ka shiga whatsApp dinka sai kaje kan Group din da kake son sakawa a wannan tsarin sai ka danne dan yatsanka.
Zai baka zabi sai ka zabi na uku 3 wato “Group Info”.
Idan ya bude sai ka shiga “Media Visibility” sai ka zabi “No”.
S…

[Cigaba] Yadda Zaka Bude Account Din Banki Ta Facebook

Image
Cigban fasaha: Shin ko kasan zaka iya bude Bank Account ta Facebook?Author: Al’amin Jamil Musa

Mai karatu barka da warhaka da fatan kana jin dadin kasancewa da mu.
Kasancewar al’amarin wannan duniya ta fuskar fasaha kullum kara gaba yake.

A yau mun zo muku da yadda zaka bude asusun ajiya na Banki wato Bank Account ta FaceBook, wannan fasahar da zata bawa mai amfani da shafin sada zumunta na Facebook damar bude asusun ajiya na banki cikin kasa da mintuna 5 ba tare da kaje banki ba.

YADDA ZAKA BUDE ACCOUNT DIN;
Nasan da daman masu amfani da Facebook messenger kan ci karo da tallan Bankin UBA wato UBA Chatting Banking.?
In kuwa haka ne kayan kaya zinke a gindi kaba.
Yadda zakai shi ne :
Zaka bukaci yin hira da shi Bankin wato “chat” kana dannawa LEO zai ma ka marhaba sannan ya tambaye ka me kake da bukata, a nan ne zaka danna opening account.
Sa su tambayeka abubuwa kamar haka:
Lambar waya
Suna
Shekarar haihuwa
Adireshinka
E-mail
Hoton ka.
Za suyi maka wadannan tambayoyi ne daya-bayan-…

Hanzarta domin yin rajista na sabon tsarin da gwamnati ta samar na P-YES bayan N-POWER.

Image
Hanzarta domin yin rajista na sabon tsarin da gwamnati ta samar na P-YES bayan N-POWER.

Presidential Youth Empowerment Scheme (P-YES) tsarine da gwamnatin Najeriya ta fito dashi domin samarwa matasa aikin yi, inda za'adauki mutun Dubu ɗari bakwai da Saba'in da hudu 774,000.

Wannan tsari ya fito ne daga ofishin sakataran gwamnatin tarayya, tare da ofishin mai temakawa Shugaban kasa na musamman akan harkokin matasa da ɗalibai.

Dan samun shiga kana bukatar abubuwa kamar haka :

1- Kazama ɗan Najeriya.
2- Kazama ɗan shekara 18 zuwa Arba'in
3- Ka iya magana da Harshan Turanci
4- Kasamu wanda ze tsaya maka (Guarantor)
5- Ka tanadi takardar shedar zama ɗan kasa ta Karamar-hukuma (Indigine Form).
6- Kazama Kanada katin zama ɗan kasa:
     National Identity Card ko
     Permanent  Voters Card (PVC) ko kuma
     International Passport


Sashin Tuntnɓa:
EMAIL ADDRESSES
info@p-yes.gov.ng
CALL CENTRE
+234 (0) 803 568 4620
+234 (0) 806 000 0399
+234 (0) 803 460 0766
+234 (0) 806 613 2217


[SABON LABARI] KUNGIYAR DALIBAI TA KASA TA BAIWA ASUU DA GWAMNATIN TARAYYA WA’ADIN ZUWA 31, DECEMBER 2018 KAN SU SULHUNTA KANSU.

Image
[Sabon Labari] Kungiyar Dalibai Ta Kasa Ta Baiwa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Zuwa 31, December 2018 Kan Su Sulhunta Kansu. Shugaban kungiyar dalibai ta kasa NANS Umar Farouq Lawal shine ya bayyana haka a yayin ganawarsa da manema Labarai yau a Abuja.
Jaridar Vanguard ta rawaito Umar Farouq ya zargin bangarorin biyu da yunkurin kawo tasgaro ga babban zaben shekara ta 2019 dake karatowa. “A yau muna so mu sanarwa da gwamantin tarayya da kungiyar ASUU cewa bama tsoron kowa, kuma mun shirya daukar matakin zanga-zangar lumana da zamu rufe filayen jiragen sama da kuma manyan hanyoyin kasar nan” “Muna jan hankalin gwamnatin tarayya ta sani cewa da yawa daga shuwagabannin kasarmu sunyi karatu a kyauta, a dai-dai lokacin damu muke biyan kudin makaranta kudin takarda da kudin wurin zama” Shugaban NANS ya kara da cewa “abun mamaki ne wasu mutane su dinga Ikrarin gwamnatin tarayya tayi wani abin azo a gani a bangaren ilimi, dai-dai lokacin da wannan abun ban takaicin ke faruwa” “Ina son wa…

Watakila mu yi watsi da Gwamnati inji Shugaban Kungiyar ASUU

Image
ASUU ta musanya maganar Gwamnati tace ba a kama shirin janye yajin aiki ba
Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya watau ASUU ta bayyana cewa babu mamaki ta daina kula gwamnatin kasar. Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi ya bayyana mana wannan a Ranar Lahadin nan a cikin Garin Legas. Farfesa Biodun Ogunyemi, ya zanta da manema labarai inda yayi jawabi game da kokarin da su ke yi na ganin an gyara harkar ilmi a kasar nan. Ogunyemi yace sun aika takardu kuma sun gana da gwamnati amma abubuwa sam sun ki gyaruwa. Kungiyar ta ASUU tace da alama ba za ta sake halartar wani zama da gwamnati ba, har sai ta nuna da gaske ta ke yi wajen cika alkawarun da ta dauka a baya. Ogunyemi ya zargi Jami’an gwamnati da kin fadawa Duniya gaskiyar abin da ke wakana. KU KARANTA: Wata kila Buhari ya karawa shugaban 'yan sanda wa'adin mulki Shugaban na ASUU yace gwamnatin tarayya ba ta da niyyar shawo karshen wannan yajin aiki da ake yi illa iyaka ta rabu da Malaman makarantar su na surutu.…

KA DUBA YANZU: {GA DAMA TA SAMU GA DALIBAN DA BASU SAMU ADMISSION BA A WANNAN SHEKARA}

Image
SAKONE DA WANI DAN UWA MAI KISHIN DALIBAI YA AIKO MANA:


Wani abu da ya kamata mutane su sani shine Garin BIU shine gari wanda yafi ko ina zaman lafiya a jihar Borno, tun daga lokacin da aka soma Boko Haram a 2009 har zuwa yanzu ba a taba kai hari garin BIU ba.

Kuma an kara tsaro na musamman saboda makarantar Nigerian Army University Biu musamman cikin makarantar sannan kuma hostels a cikin Barrack suke Jamaa idan akwai wanda yake neman admission a wata jamia bai samu ba kuma yana da 180 zuwa sama a jamb nasa to ya yi change of institution zuwa NIGERIAN ARMY UNIVERSITY BIU.

Na samu admission naga mafiya yawan daliban babu ‘yan Kano da sauran jahohin Arewa kuma makarantar sabuwa ce wannan shine karo na farko da aka soma diban dalibai kuma har yanzu suna neman dalibai saboda su samu su cika adadin da suke son diba.
Don karin bayani a shiga website nasu kamar haka :
www.naub.edu.ng

Admission list da suka saki a cikin dalibai 750 mutane 16 ne kadai daga Kano, ni kadai daga Dala L.G.A
kuma…

[KARANTA YANZU] DALILIN DA YASA DALIBI ZAICI JAMB AMMAN YA RASA SAMUN ADMISSION

Image
[Karanta Yanzu] Dalilin Da Yasa Dalibi Zaici Jamb Amman Ya Rasa Samun Admission.

Da yawa dalibai suna yin kuka da wannan matsalar cewa sunci jarrabawar Jamb amman kuma gashi basu samu admission ba, to ‘yan uwa ko kun san me yake jawo wannan matsalar?Dalilin shine:- a shekarun baya zata iya kasancewa Jamb bata baka admission ba amman makaranta sai ta baka, amman yanzu al’amarin ba haka yake ba, indai ka ga Jamb ta baka admission to tabbas makaranta ta baka haka idan jamb bata baka ba to makaranta bata baka ba.

A yanzu babu yadda za’ayi Jamb ta baka admission har sai makaranta ta baka, dama can rashin tsarina ya sanya Jamb ke bada admission ba tare da sahalewar makaranta ba.

YADDA TSARIN YAKE A YANZU SHINE:


Idan makaranta ta gama tattara Admission list dinta sai ta aikawa da Jamb, to daga nan ana sa ran Jamb zata dora sunayen daliban duka akan portal dinta, idan ta gama dorawa sai makaranta ta duba domin tabbatar da abinda ta bayar shine aka saka.

Shine sai makaranta ta fitar da nata …

Kirarin da marigayi Dan MASANIN KANO Dr Yusuf Maitama Sule, yakeyi a duk lokachin da ya halacci taro.

Image
Dan Masanin Alhaji Yusuf Maitama a duk lokacin da aka gayyace shi taro ya kan karanto wannan kirarin.

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM.
GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI, MAI KOWA, MAI KOMAI, MAI YADDA YASO,
KAN WANDA YASO, YAYIN DA YASO, A INDA YASO, KO ANA SO, KO BA A SO.

GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI MAI BAWA KOWA KOMAI, BA SHIDA BUKATAR KOMAI A GURIN KOWA, KOWA KE DA
BUKATAR KOMAI A GURINSA.

MAMALLAKIN MAMALLAK, MAI BADA MULKI GA WANDA YASO, YA FUSGE DAGA WANDA YASO, YA DAUKAKI WANDA YASO, YA KASKANTAR DA
WANDA YASO, LILLAHI WAHIDIL KAHHARI.

SARKIN DA BASHI DA NAN, BALLANTANA YAYI NAN, BASHI DA CAN, BALLANTANA YAYI CAN, A KO INA YANA NAN.

NA FARKO NE BA DA FARAWA BA, NA KARSHE NE BA DA KARSHE BA, A BAYYANE YAKE BA A GANINSA, A BOYE YAKE BA DON BAYA NAN BA.

SARKIN DA YA KASANCE TUN KAFIN KASANCE WA TA KASANCE, KUMA ZAI KASANCE BAYAN KASANCEWA TA GUSHE DA KASANCEWA.

LILLAHI WAHIDUL KAHHARI.

Allah yajikan mazan jiya.


[Ka Karanta Yanzu] Yadda Ake Yin Browsing Kyauta

Image
Yadda Ake Yin Browsing Kyauta

Ka San Free Basic? Ka San Yaya Ake Amfani Dashi?

(Yadda BUK Ta Fada Cikin Free Basics)

Menene Free Basic?
Free Basic tsarine na hadin gwiwa da shugaban kamfanin Facebook Mr. Mark Zuckerberg yayi da kamfanin Airtel a shekara ta 2013 tsarin zai baiwa al’umma damar yin facebook kyauta, shiga shafukan koyon karatu, bayanan kiwon lafiya, neman aiki, siyan kayayyaki, labarai, da kuma bincikar scholarships.

An samar da tsarin ne a kasashe masu tasowa, domin baiwa al’ummar kasashen damar cin gajiyar internet.


Daga baya aka fadada hadin gwiwar tsarin da kamfanin 9Mobile (Etisalat) yanzu kuma MTN shima ya shigo layi.

Idan kana amfani da free basic zaka iya karo wasu shafukan da zakayi amfani dasu wadanda suke cikin tsarin free basic din, Alhamdulillah yanzu haka sun sanya shafin Jami’ar Bayero dake Kano, wato dai dalibai zasu samu bayanai game da jami’ar kyauta.

Yadda Ake Amfani Da Free Basics:
Zaka iya dauko application na free basics din, ko kuma ka ziyarci shaf…

[KAYI APPLYING YANZU] HUKUMAR UNICEF TANA NEMAN MA’AIKATA A NIGERIA

Image
[Kayi Applying Yanzu] Hukumar UNICEF Tana Neman Ma’aikata A Nigeria

Hukumar lura da kananan yara ta duniya UNICEF wadda ke ayyukan jin kai da ceto ga rayuwar yara kanana, wadda a yanzu haka tana aiki a kasashe 190 na duniya tana neman ma’aikata a nan Nigeria.

Ma’aikatan da take nema sun hada da:

1. Education Sector Coordinator
*Wuri: Jihar Borno
*Ranar Rufewa: 7, January, 2019.

2. Nutrition Sector Coordinator
*Wuri: Jihar Borno
*Ranar Rufewa: 7, January, 2019.


3. WASH Officer
*Wuri: Abuja
*Ranar Rufewa: 24, December, 2018.

4. Senior Information Communications Technology Associate
*Wuri: Jihar Borno
*Ranar Rufewa: 24, December, 2018.

5. Programme Manager (Polio)
*Wuri: Borno
*Ranar Rufewa: 2nd, January, 2019.

6. Child Protection Cluster Coordinator
*Wuri: Jihar Borno
*Ranar Rufewa: 23, December, 2018.

7. WASH Cluster Coordinator
*Wuri: Jihar Borno
*Ranar Rufewa: 6, January 2018.

8. HACT Consultant
*Wuri: Ba’a fitar ba.
*Ranar Rufewa: 20, December 2018.

9. Deputy Representative, Operat…

Like us on Facebook

Leave a Reply

Name

Email *

Message *