Posts

Showing posts from January, 2019

Gargaɗi Daga NYSC Zuwa 2018 Batch "A" Corpers

Image
A shirye shiryen ta na yaye yan bautar kasa, wanda suke a rukuni na 2018  Batch "A". Hukumar NYSC ta bada wa'adi, daga yau zuwa 25 ga watan February, cewa, duk wanda ya ke da matsala ta suna ya gyara.

Wannan matsalolin sune:

Name Replacement - Sauya Suna Name Additional - Kara Suna Name Removal - Cire SunaSpelling Error - Kuskuran Harafi. Se na karshe Name Rearrangement - Canza Jerin Suna.Shiga ka ga  (NYSC CHANGE OF NAME) Yadda Za Ka Gyara Sunanka Ta Dashboard
Rashin yin haka ze bayu, wajan samun matsala a sunan da ze fito a certificate ɗin mutun. 

RUBUTU MASU ALAKA 
(INEC) Akwai Inshora Ga Dan Bautar Kasar Da Ya Samu Rauni A Lokacin Zaɓe
(Major General SZ Kazaure) Ba Wajibi Bane Dan Bautar Kasa Ya Yi Aiki Wa INEC (Adhoc Staff)
Abun Da INEC Za Ta Biya 2019 Adhoc Staffs
Kana Cikin Wanda Zasu Tafi Bautar Kasa (NYSC) Batch A 2019? Karanta Yadda Za Ka Duba Sunanka A Senate List.
(NYSC) Dan bautar kasa da aka biya shi kuɗin Allawee N198,800 amemakon 19,800(NYSC CHANGE OF NAME) Yadda Za Ka Gyara Sunanka Ta Dashboard

Image
A watan October, na Shekarar 2018 ne hukumar NYSC ta kirkiri hanyar da ɗan bautar kasa ze bi, ta dashboard ɗinsa domin gyara wannan matsalolin.

Name Replacement - Sauya Suna Name Additional - Kara Suna Name Removal - Cire Suna Spelling Error - Kuskuran Harafi Name Rearrangement - Canza Jerin Suna  Yadda Za A Gyara Shine:  Ka shiga NYSC Portal  https://portal.nysc.org.ng/nysc2/Kashigar da Email da Password ka yi log in A Dashboard ɗinka se ka danna Apply For Change Of Name  Se kazaɓa taka matsalar  Ka shiga ka gyara se ka tura musu.  Idan baka ganeba kayi comment na tambayar ka.


RUBUTU MASU ALAKA 

(INEC) Akwai Inshora Ga Dan Bautar Kasar Da Ya Samu Rauni A Lokacin Zaɓe

(Major General SZ Kazaure) Ba Wajibi Bane Dan Bautar Kasa Ya Yi Aiki Wa INEC (Adhoc Staff)

Abun Da INEC Za Ta Biya 2019 Adhoc Staffs

Kana Cikin Wanda Zasu Tafi Bautar Kasa (NYSC) Batch A 2019? Karanta Yadda Za Ka Duba Sunanka A Senate List.

(NYSC) Dan bautar kasa da aka biya shi kuɗin Allawee N198,800 amemakon 19,800Rahama Sadau Ta Kammala Digiri A Kasar Cyprus

Image
Shahararriyar yar wasan Hausar nan ta masana'antar Kannywood, Rahama Sadau ta kammala Digirinta na farko a jami'ar Eastern Mediterranean University (EMU), da ke Kasar Cyprus.

A wata tattaunawa da aka yi da ita, jarumar ta bayyana cewa, ta zaɓi ta yi karatu a jami'ar ta EMU ne, bayan binciki da ya tabbatar mata da cewa, jami'ar ta na ɗaya daga cikin manyan jami'o'i a Duniya.


Jarumar yar Shekara 25, ta shiga masana'antar Kannywood ne a shekara ta 2013, kuma ta samu karɓuwa ainun, ta karɓa lambar yabo da dama. 

A yanzun haka jarumar ta na fitowa a wasannin kudancin Najeriya (Nollywood). Kuma Producer ce a Kannywood, ita ta shirya fim ɗin Rariya. 

RUBUTA MASU ALAKA  (Ministan Ilimi Mal Adamu Adamu) ASUU Za Ta Janye Yajin Aiki
Majalisar Zartarwa Ta Kasa (FEC) Ta Amince Da Buɗe Sabbin Jami'o'i Masu Zaman kansu
ABU Zaria Ta Saki Admission
YADDA ƊALIBAN BUK ZA SU NEMI AIKIN ZABE
Wata ɗalibar ABU Zaria ta kashe kanta o

(INEC) Akwai Inshora Ga Dan Bautar Kasar Da Ya Samu Rauni A Lokacin Zaɓe

Image
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi alkawarin ɗaukar ɗawainiyar duk ɗan bautar Kasar da ya samu rauni na dindindin a ya yin zaɓe me zuwa.

Kwamishinan zaɓe na jahar Enugu Dr. Emanuel Ononamadu ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga yan bautar kasar a jahar Enugu. Ya kara da cewa, ba mu taba samun tarzomar zaɓe a jahar ta Enugu ba, kuma jami'an tsaro sun yi alkawarin kare lafiyar kowannan ku.

Kuma ya ja hankalin su akan su guji tsoma baki akan abin da ya shafi siyasa a lokacin wannan aiki, su lura da sha'anin tsaron kansu a lokacin zaɓe.


RUBUTU MASU ALAKA 

(Major General SZ Kazaure) Ba Wajibi Bane Dan Bautar Kasa Ya Yi Aiki Wa INEC

Abun Da INEC Za Ta Biya 2019 Adhoc Staffs

Kana Cikin Wanda Zasu Tafi Bautar Kasa (NYSC) 2019? Duba Yadda Za Ka Duba Sunanka A Senate List

(NYSC) Dan bautar Kasa da aka biyashi kudin Allawee 198,800 amemakon 198,800

(Ministan Ilimi Mal. Adamu Adamu) ASUU Za Ta Janye Yajin Aiki

Image
Ministan ilimi Mal. Adamu Adamu, ya bayyana cewa akwai yiwuwar Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) za su janye yajin aiki, awannan sati da zamu shiga. Ministan ya bayyana haka ne yayin da yake amsa tambayoyin yan jarida, bayan kammala wani taro a ranar Juma'a da ta gabata.

Kungiyar ta ASUU ta daka yajin ne kimanin wata biyu da suka wuce, bayan gazawar gwamnati wajan cika alkauran da ta ɗaukar musu. Hakama takwarorin su na kwalejojin ilimi, da na Fasaha su ma suna nasu yajin aikin.

Shugaban Kungiyar ta ASUU Professor Biodun Ogunyemi, ya bada tabbacin cewa Kungiyar ta su ba zata janye yajin aikin ba, mutukar gwamnati ta yi burus da bukatun nasu.

(Major General SZ Kazaure) Ba Wajibi Bane Dan Bautar Kasa Ya Yi Aiki Wa INEC (Adhoc Staff)

Image
A jawabin da ya yi wa yan bautar kasa a Port-Harcourt jahar Rivers a ayau Juma'a 25, January 2019 domin wayar musu da kai akan harkar zaɓe. Daraktan hukumar NYSC Major General SZ, Kazaure. Ya bayyana cewa ba wajibi bane yan bautar kasa su yi aiki a matsayin jami'an zaɓe na wucin gadi. Se dai su dauke shi a matsayin wata hanya ta hidimtawa kasa.

Ya yi kira agaresu da su yi koyi da mazan jiya wajan tabbatar da cigaban demokraɗiyya a kasa.

Kuma ya yi gargadi cewa duk wanda ya karya dokokin zaɓe za a hukunta shi kamar ko wana ɗan kasa.

Ya ce a shekarar 2011 da 2015 ansamu yan bautar kasar da su kayi wannan aiki, kuma mun yi alfahari da su.  Idan kun samu kanku acikin wani hali mara daɗi ku ruga zuwa
Police Station mafi kusa, ko kuma Barikin Sojoji.
Kar ku karɓa abinci, ko wata kyauta da ga yan siyasa, tsaron lafiyar ku ita ce a gaba.

Abun Da INEC Za Ta Biya 2019 Adhoc Staffs
Majalisar Zartarwa Ta Kasa (FEC) Ta Amince Da Buɗe Sabbin Jami'o'i Huɗu Masu Zaman Kansu

Image
A ranar Laraba 9, ga watan January 2019 ne majalisar Zartarwa ta Najeriya (Federal Executive Council) ta amince da buɗe Sabbin Jami'o'i masu zaman kansu (Private Universities) har guda huɗu. Shugaban kasa Muhammadu Buhari shine ya jagoranci zaman majalisar.

Ministan ilimi Mal. Adamu Adamu yayin ganawa da yan jarida ya bayyana sunayan jami'o-in kamar haka:

Greenfield University. Kaduna Dominion University.  Ibadan, Oyo Westland University.  Iwo, OsunDominion University.  Ogun 
Mal. Adamu ya bayyana cewa jami'o-in sun cika dukkanin ka'idoji kafin a sahhale musu.

Adaadin jami'o-in masu zaman kansu yanzu a Najeriya sun kai Saba'in da Tara 79.

Nigerian Navy Ta Fara Daukar Sabbin Ma'aikata 2019

Image
Hukumar Sojan Ruwa ta Najeriya ta fara dibar ma'aikata na shekarar 2019.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi 20 ga watan January 2019, a Abuja, ta bakin Daraktan yaɗa labarai na hukumar, Commodore Suleman Dahun.

Ga duk me sha'awar shiga ze iya nema ta wannan adireshi http://joinnigeriannavy.com/

Kuma ya zamana kana da mafi karancin Credit biyar, a jarabawar da bata wuce zama biyu ba ta WASCE/SSCE/GCE/NECO/NABTED, kuma kana da Lissafi da Turanci (Maths and English).

Duk wanda ze nema ya zamana ya kai shekara 18 zuwa 22, ko kuma shekara 24 zuwa 26 ga masu ND, NCE, Nursing, ko Motor Transport Department (MTD). Duk me sama da wannan sakamako ba shi da gurbi a wajan nema.

Ya zamana ba ka da aure kuma haifaffan ɗan Najeriya ne kai.

Allah ya bada sa'a.RUBUTU MASU ALAKA 

Nigerian Airforce Ta Fara Daukar Ma'aikata

Hanzarta domin yin rajista na sabon tsarin da gwamnati ta samar na P-YES bayan N-POWER.


Nigerian Airforce Ta Fara Daukar Ma'aikata

Image
Hukumar Sojan Sama ta Najeriya (Nigerian Airforce) ta fara daukar ma'aikata a matakin masu sana'ar hannu da marasa sana'a Maza da Mata (TRADES AND NON TRADES MEN/WOMEN).

Za ta fara dauka daga 12, January 2019 zuwa 23, February 2019.

Da ga cikin abubuwan da ka ke bukata:
1- Ka zama haifaffan ɗan Najeriya
2- Ka zama ɗan shekara 18 zuwa 23 (Non Trades men/women) 18 zuwa 25 (Trades men/women).
3- Ya kasance ba ka da aure
4- Ka na da tsawon 1.66 meters ko kuma 5.4 ft ga na miji. 1.63 meters ko kuma 5.3ft ga mata.....

Danna kasa dan garzaya wa shafin yanar gizo na hukumar dan karanta cikakken bayani tare da applying

http://airforce.mil.ng/page-careers
(Duba Sunanka) Nigerian Army Ta Saki Sunaye

YADDA ZAKA NEMI RANCEN KUDI N300,000 ZUWA SAMA DAGA GWAMNATIN TARAYYA –FARMER MONEY

Hanzarta domin yin rajista na sabon tsarin da gwamnati ta samar na [KAYI APPLYING YANZU] HUKUMAR UNICEF TANA NEMAN MA’AIKATA A NIGERIAP-YES bayan N-POWER.

[KAYI APPLYING YANZU] HUKUMAR UNICEF TANA NEMAN MA’…

2019/2020 Scholarship Na Islamic Development Bank

Image
Bankin cigaban Musulunci (Islamic Development Bank) da ke da headquarter a Saudiyya, da rassa a kasashen Musulmai, ya fara bada Scholarship na shekarar 2019/2020.

Su na bada Scholarship ɗin a wannan matakai :
Undergraduate Scholarship Programme
Masters Scholarship Programme
PhD Scholarship Programme
Post-Doctoral Research Programme.

Za a iya nema ta shafin yanar gizo ta IsDB http://www.isdb.org

Allah ya bada sa'a.Yi Register; Ma'aikatar Ilimi ta fara bada Scholarship na shekarar 2019/2020.

Abun Da INEC Za Ta Biya 2019 Adhoc Staffs

Image
Kamar yadda ta saba a lokacin zaɓe. Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC), a wannan Karon ma, za tayi anfani da yan bautar kasa (Copers), da kuma ɗaliban Jami'o-in Gwamnatin Tarayya, a matsayin jami'an zaɓe, domin gudanar da zaɓen shekara ta 2019.

Hukumar ta bayyana cewa, kaso Arba'in na wanda za su gudanar da zaɓen yan bautar kasa ne (Copers). Inda ta ke da mazaɓa 119,809 kuma akwai yiwuwar za ta kir kiri mazaɓa 30,000. 

Ga abin da za ta ba kowana jam'i. 
Share to copers. 

Yau Za Afara Duban Wata

Image
A wata sanarwa da ya fitar, Mai Alfarma Sarkin Musulmai, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya bada sanawar cewa, yau Lahadi 6, January 2019. Wanda ya yi dede da 29, Rabi'us Sani 1440AH. Ita ce ranar farko da za aduba sabon watan Jumada Ula 1440AH.

Ya yi umarni ga Al-ummar Musulmai, da su fara duba Jaririn watan Jumada Ula 1440AH, a yau Lahadi. Duk wanda suka gani, su sanarwa sarakunan su na Gargajiya mafi kusa da su, su kuma za su sanar wa Fada sarkin Musulmai.

Daga karshe Sarkin ya yi Addu'ar samun temakon Allah, da kuma ikon sauke hakkokin Addini ga Shugaban ni, da sauran Al-ummar Musulmi baki ɗaya.

NANABU Zaria ta saki Admission

Image
Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria (ABU) ta saki 2018/2019 UTME/DE Admission.

In kana cikin wanda suka nema,  sai ka garzaya Shafinsu na yanar gizo, (putme.abu.edu.ng) ko kuma ka danna nan ABU ADMISSION CHECKER domin ka duba naka.

Za a fara tantancewa, tare da bada Admission letters a ranar Litinin,  7, January 2019, a Mamman Kontagora Square, a main campus, daga karfe Tara na safe (9:00am)  kullun.

Ga wanda aka ba admission ga abun da zeyi :
1- Ka ɗora Olevel result ɗinka a JAMB PORTAL kafin ka je screening
2 - Se ka tafi da Original Credentials ɗinka domin tantancewa (screening) da karɓar admission.
3 - Ka leka shafin makarantar domin biyan kuɗi da kuma course registration.
4 - Sannan ka jira zuwa lokacin da za a janye yajin aiki.

Allah ya bada sa'a.

Please share.Kana Cikin Wanda Zasu Tafi Bautar Kasa (NYSC) Batch A 2019? Karanta Yadda Za Ka Duba Sunanka A Senate List.

Image
NYSC Senate List sunaye ne da makarantu suke fitarwa na wanda suka yaye, kuma suke shirin tafiya Bautar Kasa (NYSC).

Bayan makarantar ta fitar se ta turawa Hukumar NYSC,  inda su kuma suke sakawa a Shafinsu na yanar gizo. In ka duba sunanka ya na ciki to kasamu shiga cikin wadda za su tafi.

Ga yadda za ka duba :
1- Ka ziyarci shafin yanar gizo na       NYSC NYSC PORTAL
2- Ka Shiga CHECK SENATE LIST OR ITS  EQUIVALENTS.
3 - Se ka rubuta sunan makarantar
4 - Ka saka Registration/Matriculation number ka
5 - Ka shigar da sunan Mahaifi (surname)
6 - Ka shigar da shekarun haihuwarka ka (Date Of Birth)
7 - Se ka danna Search. Zai nuna ma Sunanka

Allah ya bada Sa'a.


DUBA KA GANI: MADODIN DA YA KAMATA KA ZABA (SUBJECT COMBINATION) A JARABAWAR JAMB 2019

Image
A ranar 10, ga watan January na Shekarar 2019 Hukumar shirya jarabawar shiga Jami'a (JAMB) za ta fara yiwa ɗalibai register.

Rashin zaɓar Madodin da ya kamata agurin zana jarabawar JAMB, ya na daga cikin dalilin da ya ke sawa ɗalibi ya rasa Admission ko da  kuwa ya ci JAMB, saboda Madodin da ya zaɓa ba suyi dede da abin da zai karanta a Jami'a ba.

Dan gudun samun wannan matsala duba Madar da ya kamata ka zaɓa.

Medicine and Surgery:
Use of English, Biology, Physics and Chemistry.

Agricultural Engineering:
Use of English, Mathematics, Physics and Chemistry.

Computer Science:
Use of English, Mathematics, Physics and one of Biology, Chemistry, Agric Science, Economics and Geography.

Biochemistry:
Use of English, Biology, Physics and Chemistry.

Biological Sciences:
Use of English, Biology, Chemistry and Physics or Mathematics.

Physics:
Use of English, Physics, Mathematics and Chemistry or Biology.

Mathematics:
Use of English, Mathematics and any two of Physics, Chemistry, Economic…

Duba Guraran Da JAMB ta ware domin yin register A Shekara 2019 (JAMB CBT CENTRES 2019)

Image
Hukumar shirya jarabawar shiga Jami'a ta kasa Joint Admission and Matriculation Board (JAMB), ta ware guraran da ta sahhale ɗalibi ya yi register dasu a jarabawar Shekara ta 2019.

A wannan karo Hukumar ta canza salo ne bayan la'akari da ta yi da yadda masu shagunan CAFE suke cin karan su ba babbaka. Inda suke tsugawa ɗalibai kudi.

Zuwa yanzu Hukumar ta ware gurare a dukkanin Jahohin Tarayyar Najeriya.

Domin duba wannan gurare ka danna kasa.

2019 ACCREDITED JAMB CBT CENTRES

Like us on Facebook

Leave a Reply

Name

Email *

Message *