Posts

Showing posts from February, 2019

Jahar Lagos Na Kan Gaba. Adadadin Daliban Da Suka Yi Rajistar JAMB Na Jaha Jaha

Image
Awata kididdiga da tayi, arahoton da take fitarwa na sati sati, hukumar shirya jarabawar shiga makarantar gaba da sakandare, ta bayyana adadadin ɗaliban da suka yi rajistar zana jarabawar JAMB. 

Domin samun labarai da ɗumi ɗumin su daga abun da ya shafi harkokin ilimi/manyan makarantu a Najeriya. Ayi Like ɗin Page ɗin mu na Faceboo⏩⏩Educational Updates - Hausa

Daga ranar 10, ga watan January, zuwa 15, ga watan February, akalla mutum Miliyan ɗaya da Dubu-ɗari Shida ne suka yi rajista. 
Ga kididdigar ta jaha jaha.  1. Lagos                               234,259 2. Kaduna                              99,677 3. Oyo                                     80,473  4. FCT Abuja                         73,070 5. Ogun                                  72,322  6. Kano                                  68,996 7. Rivers                                68,388 8. Plateau                              59,296  9. Nasarawa                          58,631  10. Kwara                              54,516  11. E…

Revised Academic Calendar Na BUK 2018/2019

Image
Bayan ɗage zaɓe da hukumar INEC tayi, hakan yasa manyan makarantu suka sauya jadawalin tsarin gudanar da al'amuran su na shekara. Jami'ar Bayero itama ta fitar da sabon Calendar, ayau Juma'a 22, February 2019. saɓanin wanda ta fitar kafin  ɗaga zaɓe.
Domin samun labarai da ɗumi ɗumin su daga BUK da ma sauran manyan makarantu. Ayi Like ɗin Page ɗin mu na Facebook⏩⏩Educational Updates - Hausa

Karashan abubuwan da ba'asamu yiba a calendar 2017/2018 wanda za agudanar dasu yanzu.  Sabuwar Calendar da za ayi anfani da ita 2018 /2019 
Za akammala registration a wa'annan kwanakin

Allah ya bada sa'a. 

2018/2019 Amended Academic Calendar na Kebbi State University of Science and Technology

Image
Sakamakon ɗage zaɓen 2019, ya sa manayan makarantu janza jadawalin tsarin karatu, Kebbi state university of science and technology, ta fitar da nata jadawalin ayau 21/02/2019.
FIRST SEMESTER (DATE) DURATION ACTIVITY Litinin, 11th February, 2019 – Juma'a, 1st March, 2019. Za agama registration. Sati 3
Litinin, 4th March, 2019 – Asabar, 4th May, 2019. Lectures. Sati 9.
Litinin, 6th May, 2019 – Asabar, 25th May, 2019. Jarabawar first semester. Sati 3
Lahadi, 26th May, 2019 – Lahadi, 9th June, 2019 Hutun first semester. Sati 1.

SECOND SEMESTER Litinin, 10th June, 2019 – Asabar, 10th August, 2019. Lectures. Sati 9.
Litinin, 12th August, 2019 – Asabar, 31st August, 2019. Jarabawar second semester. Sati 3.
Lahadi, 1st September, 2019 – Lahadi, 3rd November, 2019. Hutun second semester.

Litinin 4th November, 2019 Za adawo 2019/2020 Session.

Duba Admission List Na Kebbi State University Of Science and Technology

Duba Admission List Na Kebbi State University Of Science and Technology

Image
Jami'ar kimiyya da fasaha ta gwamnatin jahar Kebbi, ta saki admission na 2018/2019.
Domin duba admission ɗinka shiga kasa
http://www.ksusta.net/admissionlist?page=1


2018/2019 Amended Academic Calendar na Kebbi State University of Science and Technology

ABU Zaria Ta Saki Third Batch Na 2018/2019 Admission

Image
Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria. Ta saki third batch admission na shekarar karatu ta 2018/2019.
Domin dubawa ashiga admission portal na ABU ko ashiga ta nan
https://putme.abu.edu.ng/A saka Jamb registration number Se adanna search  🔎 Ze nuna wa mutun in yasamu 

Allah ya bada sa'a
Domin samun labarai da suka shafi ABU da ma sauran makarantu. Ayi like ɗin page ɗin mu na Facebook. Mungode

Gwamnatin Tarayya Ta Bada Hutun Zaɓe

Image
Awata sanarwa da ya fitar jiya Laraba a Abuja, Ministan cikin gida Lt-Gen. Abdurrahman Dambazau (rtd).
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bada hutun ranar Juma'a 22, ga watan February 2019. Ministan ta bakin sakatariyar dindindin na Ma'aikatar Cikin Gida, tace hutun banda ma'aikatan banki da masu ayyuka na musamman.
Gwamnatin ta bada hutun ne domin al'ummar kasa su samu garzayawa runfunar zaɓensu acikin lokaci, domin kaɗa kuri'a
Allah yasa ayi zaɓe lafiya.

Jami'o'in Da Zaka Iya Karatu Acikin Su A Najeriya Kana Daga Gida (Distance Learning Centre)

Image
Cibiyar karatu daga gida (Distance Learning Center), wani tsarine da cigaban zamani ya kawo, wanda ɗilibi ze iya karatun digiri na ɗaya har zuwa na uku ta hanyar yanar gizo, yana daga gida. Jami'ar London (University of London) ita ce makaranta ta farko da ta fara yin wannan tsari.
National Open University of Nigeria (NOUN), itace jami'a ta farko da hukumar kula da jami'o'i ta kasa (NUC) ta sahhalewa gudanar da irin wannan tsarin zalla a Najeriya. Kuma ita ce irin ta ta farko a nahiyar Afirka ta Yamma (West Africa). Yanzu haka jami'ar tana da cibiyoyi Saba'in da Biyu, a faɗin tarayyar Najeriya. 
Bayan National Open University of Nigeria,  (NOUN) hukumar ta bawa wasu jami'o'i guda Goma Shaɗaya daga cikin jami'o'in Najeriya, damar buɗe ɓangaran da zasu dinga gudanar da irin wannan tsarin na karatu. 
Ga Jami'o'in  Distance Learning Center, Ahmadu Bello University ZariaCentre for Distance Learning, University of MaiduguriDistance learning ce…

Eco Bank Nigeria Ya Fara Daukar Ma'aikata 2019

Image
Bankin Eco, ɗaya ne daga cikin bankunan yan kasuwa da suke aiki a Najeriya, kuma yana daga cikin manyan bankuna, da suke aiki a kasashan Yamnacin Afirka, Afirka ta Tsakiya, da kuma Gabashin Afirka.

Bankin a kafa shi ne a shekarar 1986, yana da rassa sama da Dubu, tare da ma'aikata sama da Dubu Goma a kasashe Talatin da Biyu, wanda suka haɗa da Benin, Burkina Faso, Burundi, Cameroon, Cape Verde, the Central African Republic, Chad, the Democratic Republic of Congo, Côte d'Ivoire, Gambia, Ghana, Guinea, Guinea Bissau, Kenya, Liberia, Mali, Malawi, Niger, Nigeria, Rwanda, Sao Tome, Senegal, Sierra Leone, Togo, Uganda, Zambia da Zimbabwe.

A yanzu haka Bankin ya fara ɗaukar ma'aikata na shekarar 2019.

Abun da ake bukata domin nema

Digiri na farko da mafi karancin sakamako na 2.2Kar awuce shekara 26 Sakamakon kammala Bautar Kasa (NYSC). 

Domin Apply danna kasa
https://workforcegroup.com/ecobank/
RUBUTU MASU ALAKA
Kanfanin Dangote Ya Fara Diɓar Ma'aikata (2019)

GTBANK TA FARA DAUK…

Yusuf Maitama Sule University, Kano. Academic Calendar Na Shekarar 2018/2019

Image
Yusuf Maitama Sule University, Kano (YUMSUK). Wacce aka fi sani da North West university. Ta saki jadawalin tsarin lokutan karatu, na shekarar 2018/2019. 
Za afara registration na sababbin ɗalibai (Fresh Students), Litinin 11, February 2019. Zuwa Juma'a 8, February 2019, tsawon sati huɗu. Dalibai masu dawowa (Returning Students), Litinin 4, March 2019, zuwa Juma'a 29, March 2019, sati uku. 
First semester za ta fara a watan March zuwa watan July 2019.  Second semester daga July zuwa November 2019. 
Karanta cikakken bayanin. 
Federal University Gusau, Ta Bada Hutun Zaɓe

Image
Jami'ar gwamnatin tarayya da ke Gusau jahar Zanfara, ta bada hutu, domin samun yin zaɓen shugaban kasa, da na yan majalisar tarayya, cikin kwanciyar hankali. 
Sanarwar ta fito ne daga ofishin yaɗa labarai na jami'ar, aranar Laraba 13, ga watan February, 2019. 
Inda hutun ze fara daga ranar Alhamis 14, ga watan February, 2019. Adawo aranar Litinin 18, ga watan February, 2019. 
Allah yasa ayi zaɓe lafiya. Federal University Dutsinma, Katsina. Ta Ba Malamai Da Dalibanta Hutu.

Image
Awata sanarwa me dauke da sa hannun registrar, na jami'ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma, jahar Katsina. Wadda ta fitar aranar Laraba 13, February 2019, amadadin shugaban jami'ar.

Federal university Dutsinma, Katsina. Ta bada hutu daga ranar Alhamis 14, February 2019, zuwa 19, February 2019. Domin kowa ya je ya sauke hakkinsa na ɗan kasa wato (Zaɓen 2019). Wanda za'ayi aranar Asabar 16, ga watan February 2019.
Za adawo ranar Laraba 20, ga watan na February 2019.
Allah ya sa ayi zaɓe lafiya.
Duba 2018/2019 Academic Calendar Na Jami'ar Bayero, Kano
University Of Maiduguri Ta Fitar Da Ranar Dawowa Daga Hutun Yajin Aiki
BUK Ta Sanar Da Ranar Fara Registration Na 2018/2019
Kano University of Science and Technology Wudil Ta Sanar Da Ranar Komawa

I

Duba 2018/2019 Academic Calendar Na Jami'ar Bayero, Kano

Image
Bayan sanarwar janye yajin aiki na kungiyar malam jami'a, wanda ta shafe watanni biyu tana yi.   Bayero University Kano, ta fitar da jadawalin tsarin karatu na Shekarar 2018/2019.  Duba ka gani. University Of Maiduguri Ta Fitar Da Ranar Dawowa Daga Hutun Yajin Aiki
BUK Ta Sanar Da Ranar Fara Registration Na 2018/2019
Kano University of Science and Technology Wudil Ta Sanar Da Ranar Komawa
Jami'ar Bayero Ta Fassara Litattafan Kimiyya Da Fasaha Zuwa Harshan Hausa

University Of Maiduguri Ta Fitar Da Ranar Dawowa Daga Hutun Yajin Aiki

Image
Awata sanarwa da ta fito daga ofishin registrer na jami'ar Maiduguri, ya bayyana cewa jami'ar zata koma karatu kamar yadda aka saba, aranar Laraba13, ga watan February 2019, bayan dogon hutu da akayi sakamakon yajin aikin kungiyar malaman jami'a wato (ASUU).
Ga sanarwar da ta fitar, karanta cikakken bayani ananRUBUTU MASU ALAKA BUK Ta Sanar Da Ranar Fara Registration Na 2018/2019
ABU Zaria Ta Saki 2018 /2019 Academic Calendar
Kano University of Science and Technology Wudil Ta Sanar Da Ranar Komawa
Sako Daga Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi

BUK Ta Sanar Da Ranar Fara Registration Na 2018/2019

Image
Jami'ar Bayero da ke Kano ta sanar da ranar da ɗalibai zasu fara registration ashirye shiryen ta na komawa zangon karatu na Shekarar 2018/ 2019.
Za afara registration daga ranar Litinin 25, ga watan February 2019 zuwa 15, March 2019, ga sababbin shiga yan 100/200 level (Fresh Students).
Dalibai masu dawowa kuma (Returning Students) daga ranar Litinin 4 zuwa 15 ga watan March 2019.
Registration yana nufin biyan kudi, tare da course registration alokaci guda.

Allah ya bada sa'a 
RUBUTU MASU ALAKA  Kano University of Science and Technology Wudil Ta Sanar Da Ranar Komawa
ABU Zaria Ta Saki 2018 /2019 Academic Calendar
Sako Daga Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi
Jami'o'i 58 Da Hukumar Jami'o'i Ta Kasa Ta Haramta (Illegal Universities)
(ABU ZARIA) Anfara Registration na 2018/2019
Jami'ar Bayero Ta Fassara Litattafan Kimiyya Da Fasaha Zuwa Harshan Hausa
Kano University of Science and Technology Wudil Ta Sanar Da Ranar Komawa

Image
Jami'ar Kimiyya da fasaha dake Wudil jahar Kano, ta sanar da ranar komawa makaranta, bayan dogon hutu da akayi sakamakon yajin aikin kungiyar malaman jami'a.
Sanarwar ta fito ne daga ofishin mataimakin registrer na makarantar. 
Duba ka gani :
RUBUTU MASU ALAKA  ABU Zaria Ta Saki 2018 /2019 Academic Calendar
Sako Daga Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi

Jami'o'i 58 Da Hukumar Jami'o'i Ta Kasa Ta Haramta (Illegal Universities)

ABU Zaria Ta Saki 2018 /2019 Academic Calendar

Image
Ahmadu Bello University Zaria ta saki jadawalin tsarin karatu na Shekarar karatu na 2018/2019.
Inda zagaye na farko ze fara daga watan February zuwa watan July 2019 (First Semester). Zagaye na biyu ze fara daga watan July ya kare awatan October 2019.
Duba ka gani Share to Abusites.RUBUTU MASU ALAKA  Sako Daga Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi
Jami'o'i 58 Da Hukumar Jami'o'i Ta Kasa Ta Haramta (Illegal Universities)
(ABU ZARIA) Anfara Registration na 2018/2019
Jami'ar Bayero Ta Fassara Litattafan Kimiyya Da Fasaha Zuwa Harshan Hausa
Usman Danfodio University, Sokoto. Dalibi Na Farko Da Ya Fita Da (First Class)
Rahama Sadau Ta Kammala Digiri A Kasar Cyprus
Majalisar Zartarwa Ta Kasa (FEC) Ta Amince Da Buɗe Sabbin Jami'o'i Huɗu Masu Zaman Kansu

Sako Daga Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi

Image
Daga ofishin registrar na jami'ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi. Sakamakon janye yajin aiki na kungiyar malam jami'a (ASUU), aranar Alhamis 7 ga watan February 2019. Jami'ar ta bada sanarwar cewa, sakamakon zaɓe da za'ayi aranar 16 ga watan February, da kuma 2 ga watan March 2019, ta ɗage komawa se bayan zaɓe.
Dalibai su zauna agida, su cigaba da bibiyar karatun su, su jira sanarwar ta gaba.RUBUTU MASU ALAKA Jami'o'i 58 Da Hukumar Jami'o'i Ta Kasa Ta Haramta (Illegal Universities)
Jami'ar Bayero Ta Fassara Litattafan Kimiyya Da Fasaha Zuwa Harshan Hausa
Usman Danfodio University, Sokoto. Dalibi Na Farko Da Ya Fita Da (First Class)
Rahama Sadau Ta Kammala Digiri A Kasar Cyprus
Majalisar Zartarwa Ta Kasa (FEC) Ta Amince Da Buɗe Sabbin Jami'o'i Huɗu Masu Zaman Kansu

Jami'o'i 58 Da Hukumar Jami'o'i Ta Kasa Ta Haramta (Illegal Universities)

Image
Hukumar kula da jami'o'i ta kasa (NUC), ta fitar da sunayan jami'o guda Hamsin da Takwas wanda suke aiki ba akan ka'ida ba. Kuma hukumar ta hana karatu awannan makarantu.
Ga sunayan su: 1. University of Accountancy and Management Studies, operating anywhere in Nigeria
2. Christians of Charity American University of Science and Technology, Nkpor, Anambra State or any of its other campuses
3. University of Industry, Yaba, Lagos or any of its other campuses
4. University of Applied Sciences and Management, Port Novo, Republic of Benin or any of its other campuses in Nigeria
5. Blacksmith University, Akwa or any of its other campuses
6. Volta University College, HO, Volta Region, Ghana or any of its other campuses in Nigeria
7. Royal University, Izhia, PO BOX 800, Abakaliki, Ebonyi State or any of its other campuses
8. Atlanta University, Anyigba, Kogi state or any of its other campuses
9. United Christian University, Macotis campus, Imo State or any of its other campuses

(ABU ZARIA) Anfara Registration na 2018/2019

Image
Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ta buɗe shafin ta na yanar gizo ayau Laraba 6 ga watan February 2019, domin registration na ɗalibai masu dawowa (Returning Students) na Shekarar 2018/2019.
Domin biyan kuɗi tare da course registration se a garzaya shafin su portal.abu.edu.ng
Haka kuma za acigaba da bada admission letter na rukuni na karshe (Last Batch) a ranar Laraba 6 ga watan na February 2019.
Allah ya bada sa'a
Please share to ABUSITE.

RUBUTU MASU ALAKA
Jami'ar Bayero Ta Fassara Litattafan Kimiyya Da Fasaha Zuwa Harshan Hausa
Usman Danfodio University, Sokoto. Dalibi Na Farko Da Ya Fita Da (First Class)
Rahama Sadau Ta Kammala Digiri A Kasar Cyprus
(Ministan Ilimi Mal. Adamu Adamu) ASUU Za Ta Janye Yajin Aiki
Majalisar Zartarwa Ta Kasa (FEC) Ta Amince Da Buɗe Sabbin Jami'o'i Huɗu Masu Zaman Kansu
ABU Zaria ta saki Admission

Kanfanin Dangote Ya Fara Diɓar Ma'aikata (2019)

Image
Dangote Group kanfanine na shahararren attajirinnan na Afirka, Alhaji Aliko Dangote. Kanfanin wanda yake da hedkwata a jahar Lagos, shine kanfani mafi girma a nahiyar Afirka baki ɗaya.  
Kanfanin anbuɗe shine a shekarar 1981, a yanzu haka yana da rassa akasashe goma na Afirka. Kanfanin ya na yin abubuwa kamar su : Siga, Siminti, Gishiri, Fulawa, Taliya da sauransu su. Anasa ran kanfanin sa na Matatar Mai (Dangote Refinery) ze fara aiki ashekara ta 2020.
Kanfanin yana da ma'aikata Dubu Talatin 30,000, kuma ayanzu haka yana ɗaukar ma'aikata. 
Domin ganin abubuwan da ya kamata ka sani kafin nema danna kasa  https://careers.dangote-group.com/Openings.aspx
Domin Nema(APPLY) shiga kasa https://careers.dangote-yigroup.com/registration.aspx

RUBUTU MASU ALAKA
 TA FARA DAUKAR MA'AIKATA 2019 (GRADUATE TRAINEE)

Nigerian Navy Ta Fara Daukar Sabbin Ma'aikata 2019

Nigerian Airforce Ta Fara Daukar Ma'aikata

Hanzarta domin yin rajista na sabon tsarin da gwamnati ta samar na P-YES bayan N…

JAMB Ta Sa Ranar Fara Jarabawar 2019

Image
Hukumar shirya jarabawar shiga jami'a (JAMB) ta bayyana ranar da za afara zana jarabawar ta Shekara 2019.
Kamar yadda hukumar ta sanar za afara zana jarabawar ne aranar 16, ga watan March, inda za za akammala aranar 23, ga watan na March.
Ko wana ɗilibi ze san ranar da ze zana tasa jarabawar, ayayin da ya fitar da slip ɗin jarabawar na karshe.
Za mu sanar awannan shafi idan lokacin ya yi
Allah ya bada sa'a.RUBUTU MASU ALAKA

DUBA KA GANI: MADODIN DA YA KAMATA KA ZABA (SUBJECT COMBINATION) A JARABAWAR JAMB 2019

Duba Guraran Da JAMB ta ware domin yin register A Shekara 2019 (JAMB CBT CENTRES 2019)


Jami'ar Bayero Ta Fassara Litattafan Kimiyya Da Fasaha Zuwa Harshan Hausa

Image
Cibiyar binciken yarukan Najeriya, fassara da al'adu ta jami'ar Bayero da ke Kano, (Centre For Research in Nigerian Languages, Translation and Folklore), ta fassara Litattafan Kimiyya guda Takwas da yaran Hausa, domin anfanin makarantun firamare, kanana da manyan makarantun sakandare, na Arewacin Najeriya.
Daraktan cibiyar Professor Aliyu Mu'azu ne ya bayyana haka, yace Litattafan sune:
Kimiyya da Fasaha don makarantun firamare, Littafi na ɗaya zuwa na uku Lissafi don kananan makarantun sakandare, littafi na ɗaya zuwa na uku Kyamistare don manyan makarantun sakandare Fizis don manyan makarantun sakandare. 
Daraktan ya bayyana cewa hakan ya biyo baya ne, sakamakon yunkurin da cibiyar ta yi wajan ganin ta tallafawa cigaban  ilimin zamani ta hanyar yin amfani da yaran uwa a arewacin Najeriya.  Yace duk kasashan da suka cigaba za kasamu da yaransu suke karantarwa, wannan shine sirrin cigaban kasa. 
Shugaban jami'ar Professor Yahuza Bello ya yi alkawarin tallafawa duk wani …

GTBANK TA FARA DAUKAR MA'AIKATA 2019 (GRADUATE TRAINEE)

Image
Bankin Guaranty Trust ya fara ɗaukar ma'aikata na Shekara ta 2019.
Bankin Guaranty Trust, ɗaya ne daga cikin bankunan da suke aiki a kasashan Yamnacin Afirka, Afirka ta Tsakiya, da kuma kasashan Turai.
Ayanzu haka Bankin ya na juya sama da kimanin Naira Triliyan Uku da ɗugo Goma Shaɗaya N3.11Trilion. Kuma yana da ma'aikata sama da Dubu Goma 10,000,  akasashan  Nigeria, Cote - D'Ivoire, Gambia, Liberia, Kenya, Ghana, Uganda, Rwanda, Tanzania, Sierra Leone da kuma United Kingdom.
Takyan Aiki : Graduate Trainee Gurin Aiki : Dukkan Garuruwan Najeriya
Abubuwan Da Ake Bukata
Mafi karanci, Digiri na farkoCredit Biyar tare da Turanci da Lissafi (Maths and English) Sakamakon kammala hidimar kasa (NYSC) 
Shekaru Kar mutun ya wuce shekara Ashirin da Shida 26.
Za Arufe Dauka 06/02/2019
Shiga nan kayi Apply APPLY HERERUBUTU MASU ALAKA

Nigerian Navy Ta Fara Daukar Sabbin Ma'aikata 2019

Nigerian Airforce Ta Fara Daukar Ma'aikataUsman Danfodio University, Sokoto. Dalibi Na Farko Da Ya Fita Da (First Class)

Image
A karon farko, tsangayar Kimiyyar Binciken Kasa (Geology), na jami'ar Usman Danfodio da ke sakkwato, ta yaye ɗilibi da sakamako me daraja na farko (First Class).


Abdullahi Aminu Al-ameen, Shine ɗilibi na farko da ya fita da First Class, tun bayan kafa tsangayar a Shekara ta 2013. 

Abdullahi Aminu Al-ameen ɗan asalin jihar Kebbi ne, ya fita da maki 4.54 CGPA. Kuma ya fara sha'awar karanta wannan fannin ne tun yana makarantar Sakandiri. 


RUBUTU MASU ALAKA 
Rahama Sadau Ta Kammala Digiri A Kasar Cyprus
(Ministan Ilimi Mal. Adamu Adamu) ASUU Za Ta Janye Yajin Aiki
Majalisar Zartarwa Ta Kasa (FEC) Ta Amince Da Buɗe Sabbin Jami'o'i Huɗu Masu Zaman Kansu
ABU Zaria ta saki Admission
Like us on Facebook

Leave a Reply

Name

Email *

Message *